Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Sweden Ta Yi Alkawarin Karin Tallafin Sojoji Ga Ukraine

0 176

Sweden za ta aika wa Ukraine wani sabon kunshin tallafin soji da darajarsu ta kai kambi biliyan 2.2 (dala miliyan 199) wanda ya kunshi harsasai na manyan bindigogi kuma tana duban aika jiragen yaki, in ji Ministan Tsaro Pal Jonson.

 

Jonson ya shaidawa wani taron manema labarai cewa a ranar 6 ga watan Nuwamba ne rundunar sojin kasar za ta bayar da rahoto kan yiwuwar aikewa da jiragen saman Jas Gripen zuwa Ukraine bayan da gwamnatin kasar ta bukaci su tantance lamarin.

 

Sai dai kuma ya nanata cewa Sweden saboda dalilan tsaro na cikin gida na bukatar zama memba a kungiyar tsaro ta NATO kafin ta samu damar kare duk wani jiragen yaki.

 

Sweden na fatan shiga kungiyar tsaro ta NATO nan ba da jimawa ba ko da yake kasashen Turkiyya da Hungary sun amince da shigarta.

 

Sabon kunshin taimakon na soji zai kasance na 14 na Sweden ga Ukraine tun bayan mamayar Rasha, wanda ya dauki jimillar kudaden taimakon da kasashen Nordic ke bayarwa sama da rawanin biliyan 22.

 

“Muna buƙatar tsara tallafinmu domin ya daɗe kuma ya dore,” in ji Jonson.

 

“Yanzu yana da mahimmanci kasashe da yawa su tashi tsaye don tallafawa Ukraine.”

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *