Take a fresh look at your lifestyle.

Mutane Hudu Suka Mutu A Hadarin Jirgi Sama A Ostireliya

0 96

Wani karamin jirgin sama ya yi hatsari a wani kauye na jihar New South Wales ta kasar Australia inda ya kashe matukin jirgin da yara uku da ke cikin shi, in ji ‘yan sanda.

 

Jirgin Cirrus SR22 ya tashi daga Canberra kuma ya fado da misalin karfe 3 na yamma. lokacin gida (0400 GMT) kusa da garin Queanbeyan wanda ke da nisan kusan kilomita 290 daga Sydney.

 

Jami’an bayar da agajin gaggawa sun mayar da martani kan rahotannin da ke cewa wani jirgin ya yi hatsari kuma yana ci da wuta, inda jami’an kashe gobara suka kashe gobarar amma babu wanda ya tsira, kamar yadda ‘yan sanda suka ce.

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *