Take a fresh look at your lifestyle.

Isra’ila Ta kashe Mutane Da Dama A Wani Hari Kan Sansanin ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu

0 288

Jami’an kiwon lafiya a Gaza sun ce Falasdinawa da dama ne suka mutu tare da jikkata sakamakon harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia.

 

Ministan tsaron Isra’ila ya ce zirin Gaza zai shiga cikin “halin kakani kayi gaba daya” ciki har da hana shigar abinci da mai.

 

Wannan kazamin harin bam ya zuwa yanzu ya raba mutane fiye da 120,000 da muhallansu a yankin Falasdinawa da aka yi wa kawanya.

 

Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta 100,000 ne suka taru a kusa da Gaza, inda mayakan Falasdinawa suka ce suna tsare da mutane 130.

 

Adadin wadanda suka mutu na baya-bayan nan ya kai Falasdinawa 560 a Gaza, a cewar Jami’an lafiya.

 

Harin ba-zata na Hamas ya zo ne bayan da Isra’ilawa ‘yan kawanya suka kai hari a Masallacin Al-Aqsa a ‘yan kwanakin nan kuma Isra’ila ta kashe Falasdinawa da dama a ‘yan watannin nan.

 

 

 

ALJAZEERA/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *