Take a fresh look at your lifestyle.

Kowa Yana Da Alhaki Akan Ilimin Yara Mata Da Kyautata Rayuwa – Kakakin Abbas

0 239

Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya ce a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ‘ya’ya mata ta duniya a yau, duk masu ruwa da tsaki na da rawar da za su taka ta fuskar ilimi da bunkasar su da kuma walwala.

 

Shugaban majalisar ya bayyana cewa, cibiyoyin ilimi, addini da na gargajiya, da kuma gwamnati na da rawar da za su taka wajen ba da kariya, renon yara da kuma ci gaban kwakwalwar ‘ya’ya mata da sauran yara baki daya.

 

Kakakin majalisar Abbas ya kuma yi Allah-wadai da yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, kamar yadda ya yi Allah-wadai da yawaitar ayyukan yi wa yara fyade da cin zarafin yara.

 

Shugaban majalisar ya ce zai zama alfanu ga al’umma gwamnatoci a kowane mataki su mayar da ilimi musamman a matakin firamare kyauta kuma ya zama wajibi ga yara.

 

Shugaban majalisar ya sake nanata shirye-shiryen majalisar ta 10 na ba da goyon bayan majalisa ga duk wani shiri ko manufofin da aka tsara don kyautata rayuwar ba yarinya kadai ba har ma da dukkan yara a fadin kasar.

 

A ranar 19 ga Disamba, 2011, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kuduri mai lamba 66/170 na ayyana ranar 11 ga Oktoba a matsayin ranar yara mata ta duniya, don amincewa da ‘yancin ‘yan mata da kalubale na musamman da ‘yan mata ke fuskanta a duniya.

 

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, ranar ‘ya’ya mata ta duniya ta mayar da hankali ne kan bukatar magance kalubalen da ‘yan mata ke fuskanta da inganta karfafa ‘ya’ya mata da kuma biyan hakkokinsu.

 

Yayin da yake lura da cewa alhakin ya fara ne daga iyaye, musamman da tarbiyyar ‘ya mace, Kakakin Abbas ya kara da cewa dole ne al’umma baki daya su tabbatar da tsaro da tarbiyyarsu.

 

Bugu na wannan shekara mai taken: ‘Sanya Zuba jari a ‘Yan Mata: Jagorancin Mu, Jin Dadin Mu.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *