Wata kotu a Indonesiya a yau litinin ta yi watsi da kararraki da dama da ke neman sauya dokokin cancantar ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa.
Kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukunci kan wasu jerin kararraki irin wannan a ranar Litinin din da ta gabata, a daidai lokacin da ake ci gaba da sukar abin da majiyoyi ke cewa kokarin da shugaba mai barin gado Joko Widodo keyi na gina daular siyasa tare da ci gaba da rike madafun iko bayan ya bar mulki.
Demokradiyyar kasa ta uku mafi girma a duniya za ta kada kuri’a a zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisa a lokaci guda a ranar 14 ga Fabrairun shekara mai zuwa.
Alkalin Alkalai Anwar Usman, wanda surukin shugaban kasa ne, kuma ke jagorantar kwamitin da ya kunshi alkalai tara, ya ki amincewa da bukatar rage mafi karancin shekaru zuwa 35 daga 40 da kuma ba duk wanda ke da kwarewar aikin gwamnati damar tsayawa takarar shugaban kasa da mataimakinsa.
Alkalan sun ce kayyade shekarun ya rage ga ‘yan majalisa kuma karar ba ta da “dalili bisa doka”.
Idan har an amince da koken zai baiwa dan shugaban kasa kuma magajin garin Surakarta, Gibran Rakabuming Raka damar tsayawa takara a zaben watan Fabrairu mai yuwuwa a matsayin abokin takara.
Gibran bai amsa bukatar yin sharhi nan take ba.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply