Babban mai horar da kungiyar Gombe United, Baba Ganaru, ya ce har yanzu kungiyar shi na cikin lokacin da za ta gyara duk da wasn da kungiyar ta Shooting Stars Sports Club (3SC) ta yi a ranar Lahadi.
Kungiyarsa ta yi rashin nasara da ci 1-2 a hannun 3SC mai masaukin baki a gasar Premier League ta Najeriya ta 2023/2024 da aka buga a filin wasa na Lekan Salami da ke Badun.
Ganaru ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala wasan, bayan kammala wasan, ya ce an hada kungiyar ta Gombe United ne makonni takwas kacal da suka wuce.
“Na shiga kungiyar makonni biyu kafin a fara gasar kuma dukkan ‘yan wasan sun bar kungiyar. Masu tsaron gida uku ne kawai da ‘yan wasa hudu a filin wasa.
“Har ila yau, ba mu da lokacin da za mu buga wasannin share fage da na gwaji da yawa,” in ji shi.
Kociyan ya bayyana jin dadin shi kan kokarin da ‘yan was an shi suka yi a wasan na ranar Lahadi.
“Kungiyar sabuwa ce, kuma na yi imanin kungiyar tana inganta yayin da muke ci gaba a gasar.
“Sa’an nan za mu dauki kowane wasa kamar yadda ya zo kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen shirye-shiryen mu da Bendel inshora a was an mu na gaba,” in ji shi.
Ganaru ya kara jaddada bukatar yin alkalanci mai kyau da inganci a wasannin gida da waje domin daukar gasar lig ta Najeriya zuwa ga kololuwa.
“Jami’an wasan ba sa taimakawa al’amura idan ana maganar wasannin waje a Najeriya.
“Rashin alƙalan wasa yana sa ‘yan wasa da magoya bayan shi su daina amincewa kuma su yi imanin cewa babu wani abin dogaro a gasar ta gida.
“Saboda rashin yin alkalanci, musamman a wasannin waje, ‘yan wasa ba sa bayar da mafi kyawun su. Wasu daga cikinsu ba za su so yin kasada ba, yayin da wasu ke nuna fargaba,” in ji shi.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply