Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bude taron koli na BRI karo na 3 a hukumance a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.
An fara bikin bude taron da karfe 10:00 na safe agogon kasar, a babban dakin taron jama’a na birnin Beijing.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, shi ne ke wakiltar shugaba Bola Tinubu a wajen taron.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin yana halartar taron.
A jawabin shi na bude taron, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, shirin na Belt da hanyoyi yana nufin inganta cudanya don yin hadin gwiwa cikin lumana a duniya baki daya.
Ya sanar da tsare-tsare daban-daban da kasar Sin ta gindaya na fadada shirin samar da hanyoyina yankuna.
A karshen bikin bude taron Najeriya za ta gudanar da tattaunawa tsakanin kasashen biyu da za ta kai ga rattaba hannu kan yarjeniyoyin da za su bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari a kasar.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply