Gwamnan Katsina Ya Nemi Gudummuwar Malaman Addini Wajen Magance Matsalar Tsaro A jihar
Kamilu Lawal,Katsina.
Gwamnan jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya, malam Dikko Umaru Radda ya bukaci malaman addini su dukufa wayar da kan jama’a akan damar da addini ya bada domin hada kai wajen kare kai daga masu kawo harin ta’addanci da cin zarafin al’umma.
Ya bukaci malaman da cewa a duk lokacin da suke gabatarwa a wani majalisi ko bayar da karatu su jaddadawa mabiya halarcin tashi tsaye wajen kare kai daga wulakanci da cin zarafin daga maharan.
Gwamna Radda yayi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron wa’azin kasa wanda kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’a wa’ iqamatus sunnah ta kasa (JIBWIS) ta shirya a jihar Katsina.
Ya nemi addu’a ga sabbin matasan sintirin na“Jami’an Sanya Ido na Alumma” wadanda gwamnatin jihar ta kaddamar domin su kare yankuna da garuruwan da suka fito bayan da gwamnatin ta horas dasu tare da basu kayan aikin da suke bukata.
“Muyi wa matasan nan namu addu’a, Allah Ya basu nasara akan yan ta’adda domin kawo karshen ta’addanci da cin zarafin al’ummar mu”, Dikko Radda yace.
Ya kuma jaddada matsayin gwamnatin na cewa ba za tayi sasanci da yan ta’adda ba, yana mai fatan samun nasarar matakan gwamnatin jihar na kawo karshen matsalar tsaron a jihar nan bada jimawa ba.
Gwamnan ya kuma bukaci al’umma da su binciki ayyukan su tare da tuba zuwa ga Allah domin neman samun dauki daga Allah.
“Mu binciki halaye da ayyukan da muke yi tsakanin mu da Allah kuma mu nemi gafarar shi domin ya kawo mana dauki tare da bamu nasara akan ‘yan ta’addan da muke fama dasu”, inji shi.
Kamilu Lawal.
Leave a Reply