Fada ya sake barkewa a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango tsakanin dakarun da ke goyon bayan gwamnati da ‘yan tawayen kungiyar M23.
Mazauna yankin sun ce ‘yan tawayen sun mamaye garin Kitshanga da ke lardin Kivu ta Arewa tun ranar Asabar.
An kai mutane da dama asibiti da raunukan harbin bindiga, kamar yadda wani gidan rediyon kasar ya ruwaito.
“‘Yan tawayen suna Kitshanga kuma muna kokarin nemo hanyar da za mu kwato garin,” in ji wata majiyar tsaro.
Yankin ya canza hannu sau da yawa tun farkon shekara.
Fadan dai ya sake barkewa makonni uku da suka gabata bayan tsagaita bude wuta na tsawon watanni shida. A baya dai dakarun kasa da kasa ne ke sintiri a yankin da makwabtan Kwango suka samar.
BBC/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply