Take a fresh look at your lifestyle.

GWAMNATIN JIHAR KWARA ZATA BUNKASA AIKIN NOMA DUK SHEKARA

0 115

Gwamnatin jihar Kwara ta ce a shirye ta ke ta inganta ayyukan noman duk shekara domin tabbatar da samar da abinci mai yawa a jihar.

 

Kwamishinan aikin gona na jihar Malam AbdulLateef Alakawa ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi ragamar jagorancin Cibiyar Injiniya ta Aikin Gona ta Najeriya (NIAE) a Ilorin, Jihar Kwara.

 

Kwamishinan ya bayyana cewa jihar ta sake sabunta kudirin ta na samar da dorewar noma na kasuwanci, inda ya ce kwara ta riga ta fara aiwatar da tsare-tsare da suka dace da manufa.

 

Alakawa ya lura cewa injiniyoyin aikin gona na da muhimmiyar rawar da zasu taka wajen bunkasa noma a jihar.

 

Kalamansa: “Gudunwar injiniyoyin aikin gona wajen samar da abinci da kuma darajar sa a cikin kasa na da matukar muhimmanci. A matsayinmu na Jiha mun dauki matakin bunkasa kwazon masu ruwa da tsaki a fannin kamar injiniyoyi da jami’an tsawaita. Hakazalika, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta sayo sabbin manyan motoci guda biyu da taraktoci 15 domin inganta injina, nan ba da jimawa ba za mu kaddamar da na’urorin ban ruwa,” inji shi.

 

Alakawa ya kara da cewa gwamnatin jihar ta share fili mai fadin hekta 100 a Agbeyangi, karamar hukumar Ilorin ta Gabas a wani bangare na shirinta na Farm Kwara Initiative, inda ya kara da cewa an sake raba wani kadada 500 na fili a Adanla da ke karamar hukumar Ifelodun saboda haka.

 

A cewarsa, gwamnatin jihar ta nuna aniyar yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da manufofinta na noma mai dorewa.

 

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar NIAE na kasa Farfesa Akindele Alonge, ya yabawa gwamnatin jihar Kwara karkashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bisa nasarorin da ta samu a fannin noma.

 

Agro Nigeria

Leave A Reply

Your email address will not be published.