Motocin agaji 17 ne suka shiga yankin zirin Gaza daga kasar Masar a ranar Lahadin da ta gabata, domin ba da taimako ga yankin Falasdinu, wanda Isra’ila ke fama da hare-haren bama-bamai da kuma kawanya tun farkon rikicin Hamas.
A ranar Asabar, bayan ayarin motocin farko na manyan motoci 20 suka wuce, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kayan ya yi daidai da kashi 4 cikin 100 na kayayyakin da ake shigowa da su Gaza a kullum kafin a fara yakin. Har ila yau, sun bayyana cewa, za a bukaci akalla manyan motoci 100 a kowace rana ga mutanen Gaza miliyan 2.4, wadanda rabinsu yara ne, wadanda ba su da kayan masarufi.
Africanews/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply