Take a fresh look at your lifestyle.

Horar Da Malamai: Kungiyar EU Za Ta Tallafa Wa Arewa Maso Gabashin Najeriya Da Yuro Miliyan 5.4

0 114

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta sanar da saka hannun jarin karin Yuro miliyan 5.4 domin bunkasa kwazon malamai a yankin Arewa maso Yamma.

 

 

Kwamishiniyar hadin gwiwa ta kasa da kasa ta EU Jutta Urpilainen ce ta bayyana haka a wajen kaddamar da shirin bada tallafin kudi na Euro miliyan 4 kan harkokin ilimi da karfafa matasa a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ta hanyar shirin Global Gateway.

 

A cewar Urpilainen, zuba jarin ya yi daidai da kudurin kungiyar EU na dakile yawan yaran da ba su zuwa makaranta a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ta hanyar inganta samar da ilimi mai inganci da kuma karfafawa matasa a yankin.

 

 

“Wannan bangaren yana cike da wani shiri na daban na Euro miliyan 5.4 da muka sanya wa hannu a yau, wanda aka sadaukar da shi ga malamai don burin gina juriyarsu da karfinsu a cikin yanayi masu wahala.

 

 

Dole ne mu tuna cewa babu ilimi ba tare da malamai ba don haka ne ma ya zama dole mu saka hannun jari a horar da malamai.

 

 

Buri na uku na shirin namu shi ne, hakika yana ba wa matasa kwarin gwiwa da dabarun da suke bukata, wajen samar da ilimin sana’a.

 

 

Wannan gagarumin shirin da aka kaddamar a yau an tsara shi ne tare da hukumomin Najeriya don tabbatar da mallakarsu da kuma samar da isasshiyar amsa ga bukatun cikin gida,” inji ta.

 

 

Urpilainen ya ce Najeriya ba ita ce kadai mai karfin tattalin arziki a Nahiyar ba, kuma ita ce kasa mafi yawan al’umma a Afirka, har ma ta kasance babbar abokiyar kawancen Tarayyar Turai a yankin Yamma.

 

 

Don haka ta ce shirin zai mayar da hankali ne wajen fitar da yaran makaranta daga kan titi domin samun ilimin da ake bukata musamman ‘ya’ya mata ta bangarori daban-daban.

 

 

Urpilainen ya ce an kuma tsara shirin ne don ba da taimako kai tsaye ga iyalai, musayar kuɗi, kariyar zamantakewa, samar da kuɗin shiga, kyauta da taimako ta hanyar ayyukan noma.

 

 

Da yake mayar da martani a madadin Gwamnonin Arewa maso Yamma, Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya yabawa Kungiyar Tarayyar Turai kan tallafawa yankin.

 

 

“Jihohin Arewa maso Yamma su ne suka fi yawan al’umma a kasar nan, don haka wannan tallafin na zuwa a daidai lokacin da ya dace.

 

 

Ga kowane ɗayanmu ilimi shine fifiko kuma mun yanke shawara tare da ɗaiɗaiku don saka hannun jari a fannin ilimi kuma a shirye muke mu canza labarin nan da shekaru huɗu masu zuwa.”

 

 

Ministan Ilimi Tahir Mamman ya ce ilimi shi ne mabudin ci gaba don haka akwai bukatar a baiwa matasa damar samun nasara.

 

 

“Idan ba a bai wa matasanmu tarbiyya yadda ya kamata ba, ba a horar da su da kuma karfafa su ba, muna wasa ne da makomar kasar nan. Rashin ciyar da su zai ba da damar talauci ya karu kuma rashin tsaro ya bunkasa.”

 

 

Mamman ya yi kira ga Gwamnonin Jihohin da su mayar da hankali wajen ba da fifiko kan ilimi da karfafawa matasa, ya kara da cewa taswirar fannin ilimi da za a fitar nan ba da jimawa ba ya kunshi manufofin Tarayyar Turai na sake fasalin fannin.

 

 

Ya ce abin da Ma’aikatar ta mayar da hankali a kai shi ne komawa ga ilimi na asali don magance yaran da ba sa zuwa makaranta, ‘yan mata masu tasowa wadanda ke bukatar a horar da su da kuma karfafa su.

 

 

Ya kara da cewa gwamnati a shirye ta ke ta aiwatar da kashi 25 na kasafin kudin a fannin ilimi.

 

 

“Dukkan abin da Shugaban kasa ke bukata, a cewarsa, manufofi ne da za su tabbatar da kasafin kudin kuma abin da muke aiki a kai ke nan,” in ji Mamman.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *