Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh ya ce neman ‘yancin cin gashin kai da Falasdinawa ke yi ba zai tsaya ba ba tare da la’akari da ayyukan Isra’ila ba.
Shtayyeh ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a gaban zaman majalisar ministocin kasar a Ramallah a yankin yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye, inda ya ce yawan mace-macen na barazana ga dubban yara da marasa lafiya a asibitocin Gaza yayin da man fetur ke karewa kuma ana fama da karancin wutar lantarki da ruwa da magunguna da kuma abinci.
“Mutanen mu da ke Zirin Gaza suna fuskantar kisan kai daga Isra’ila,” in ji shi.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply