Take a fresh look at your lifestyle.

Hare-Haren Bama-baman Isra’ila A Gaza: Shugabannin Duniya Sun Yi Kira Da A Daina

3 129

Sojojin Isra’ila sun tsananta kai hare-hare a kudancin Gaza cikin dare bayan daya daga cikin ranaku mafi muni ga Falasdinawa tun bayan barkewar rikici a daidai lokacin da shugabannin kasashen duniya suka yi kira da a dakatar da yakin domin ba da damar kai agaji cikin yankunan da aka yiwa kawanya.

 

Yayin da ake fargabar rikicin Isra’ila da Hamas zai bazu a Gabas ta Tsakiya, Rundunar Sojin Isra’ila ta ce jiragenta sun kai hari kan ababen more rayuwa na Sojojin Siriya da harba turmi.

 

Amurka da Rasha ne ke jagorantar kiraye-kirayen kasa da kasa na a dakatar da fada tsakanin Isra’ila da Hamas domin ba da damar kai agaji cikin Gaza inda Falasdinawa ke rayuwa cikin mawuyacin hali.

 

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 704 da suka hada da kananan yara 305 a ranar Talata, adadin da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce shi ne mafi girma da aka bayar a rana guda tun bayan barkewar rikici kusan makonni uku da suka gabata. .

 

Akalla Falasdinawa 5,791 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.

 

Fiye da yara 2,000 na daga cikin mutane 5,791 da aka kashe a Gaza a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.

 

Yayin da suke gabar yammacin kogin Jordan, sama da Falasdinawa 100 ne sojojin Isra’ila suka kashe tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya ta Falasdinu.

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

3 responses to “Hare-Haren Bama-baman Isra’ila A Gaza: Shugabannin Duniya Sun Yi Kira Da A Daina”

  1. бисермен жұмыс ашық сабақ, бисер жасау tabys регистрация,
    tabys курьерская служба сұрақтарға жауап беріп тапсырманы орындаңдар, 6 тапсырма
    сұрақтарға жауап бер ертіс
    өзені 1 положительная группа крови характер, 3 группа крови характер мужчины

  2. синастрия уран и узлы лунный день для увольнения, благоприятные дни
    для увольнения с работы в 2024 году академия магии звездной
    к чему снится беременная и родила ребенка
    синяк на ноге приснилось

  3. магнитная индукция движущегося заряда формула, движение заряженных
    частиц в магнитном поле шығыстың қос шынары эссе, шығыстың қос шынары тақырыбында бірлескен жоба арғымақ ат, арғымақ
    әбіш кекілбаев артериялық гипертензия
    kazmedic, артериялық гипертензия алғашқы көмек

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *