Rikicin Falasdinu Bashi Da Nasaba Da Addini Ko Kabilanci: Jakadan Falasdin A Najeriya
Musa Aminu, Abuja
Jakadan Falasdin a Najeriya Abdullah Shawesh ya yaba bisa yadda kasar sa ke Kara samun goyon baya daga wasu kasashen Duniya,
Jakadan, ya yi wannan furucin ne yayin taron manema labarai da ya kira a Abuja babban birnin Najeriya ranar larabar nan.
Ya cigaba da cewa wannan
” wannan rikici ya yi sanadiniyar mutuwan kimanin Yan kasar Falasdinu 6000 a wani kididdiga da ka fitar ranar bakwai ga watan Octoban nan wadanda suka mutun kuwa sun hada da mata da kananun Yara, yayin da Mutum 1800 suka samu rauni”
Ya Kara da cewa rikicin bashi da nasaba da addini ko kabilanci Kana ba rikicin ne tsakanin Isra’ila da hamas ba, illa kawai karantsana ne mai alaka da siyasa da ake yiwa kasar sa ta Falasdinu.
Kazalika, Ya yi Allah wadai da yadda wasu shugabannin kasashen Duniya ke rububin kai ziyara tare da ayyana goyon bayansu ga kisan kare dangi da a cewar sa a ke yi wa al’ummar Falasdinu, baya ga taimakawa da su ke yi a lamarin ta fuskar kayan yaki.
Ya Kuma bayyana dokokin kasa da kasa a matsayin hanya daya tilo da za a iya kawo karshen wannan cin zarafin na Dan Adam tare da kisan kare dangi.
Tun da fari dai jakadan na kasar Fasdinu a Najeriya Abdullah Shawesh ya zargi kafafen yada labaran kasashen yamma da sake rura wutar rikicin, inda ya bukaci manema labarai a Najeriya da su basu goyon baya a kokarin da suke yi na wayar da kan jama’a dangane da halin da ake ciki a kasar ta Falasdinu ya Kuma ce a Shirye yake da ya amsa gayyatar manema labarai a Koda yaushe domin warware zare da abawa dangane rikicin.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply