Kafofin yada labarai na kasa da kasa da kungiyoyin agaji sun ce sun rasa hulda da ma’aikatan su a Gaza sakamakon katsewar hanyoyin sadarwa a yayin da hare-haren da Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza ya kara tsananta.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce sojojinta na kasa suna “fadada ayyukan” a yankin Gaza.
Fiye da yara Falasdinawa miliyan 1 da iyayensu suna rayuwa cikin “tatsuniyar tsoro” a cikin yankin da aka yi wa kawanya, in ji kungiyar agaji ta Save the Children.
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da ba shi da tushe balle makama da ke neman a yi sulhu.
Akalla Falasdinawa 7,326 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply