Majalisar dattawan Amurka a ranar Alhamis din nan ta yi watsi da dokar da za ta tilastawa shugaba Joe Biden janye sojojin Amurka daga Nijar, kasar da ke yammacin Afirka inda jami’an soji suka kwace mulki a watan Yuli. 86-11 sun ki amincewa da matakin.
Sanata Rand Paul, dan jam’iyyar Republican, wanda ya dauki nauyin wannan doka, ya bayar da hujjar cewa, an tura sojojin ne ba bisa ka’ida ba, ba tare da amincewar majalisar dokokin kasar ba, ya kuma ce bai kamata Amurkawa su kasance cikin kasadar shiga cikin rikicin Nijar ba.
“Gaskiya Gabas ta Tsakiya na cin wuta, wace ma’ana ce a ce akwai sojoji sama da 1,000 a Nijar? Shin yana da ma’ana a kafa dakaru sama da 1,000 a kasar da gwamnatin mulkin soji ke mulki? In ji Paul a cikin jawabin majalisar dattijai.
Shugaban jam’iyyar Democrat na kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattijai Sanata Ben Cardin, ya ce idan Amurkawa suka janye, za ta iya barin wani gibi da Rasha ko abokan hayar ta Wagner za su iya cikawa.
“Ba ma ba da isasshen hankali ga wannan ɓangaren na duniya. Tabbas ba ma son nuna alamar cewa muna watsi da wannan bangare na duniya, “in ji Cardin.
Amurka ta bayyana a hukumance a wannan watan cewa an yi juyin mulkin soja a Nijar, wanda ya haifar da dakatar da taimakon a hukumance, amma jami’an Amurka sun ce babu wani shiri na sauya yawan sojojin Amurka a kasar.
Nijar ta kasance abokiyar kawance don yakin Washington da masu tayar da kayar baya da suka kashe dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu a Afirka. Akwai kimanin jami’an ma’aikatar tsaro 1,000 a kasar.
Reuters/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply