Take a fresh look at your lifestyle.

Gwammatin Tarayya Ta Himmatu Wajen Farfado Da Bangaren Sarrafa Karafa.

Musa Aminu, Abuja.

0 111

Gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin sake gyara harkar sarrafa karafa a Najeriya domin habaka tattalin arziki, da samar da ayyukan yi don gaggauta bunkasar masana’antu.

Ministan Kasa a ma’aikatar karafa ta Najeriya, Uba Maigari Ahmadu ne ya bayyana haka a wata ziyarar aiki da ya kai jihar Anambra.

A yayin ziyarar, Ministan ya kai ziyarar aiki ga Gwamna Chukwuma Soludo a gidan Gwamnan dake garin Amawbia.

Ministan ya ce yana alfahari da Gwamna Soludo kuma ya aminta da jihar Anambra a matsayin cibiyar ci gaban masana’antu a kasar, sannan ya bayyana goyan bayansa ga gwamnatin jihar.

Da yake karbar Ministan, Gwamna Soludo ya yabawa gwamnati mai ci bisa yadda suka sanya hannunsu a kan muhimman abubuwa, inda ya bayyana fatan cewa gwamnati mai ci za ta samar da tsare- tsaren da za su kai ga cin moriyar manyan damamarmakin da kasar ke da su.

Tun da farko ministan ya yi rangadi a cibiyar horar da harkokin sarrafa karafa MTI, dake garin Onitsha, inda ya koka kan yadda matasan Najeriya ke hankoron samun takardun kammala karatu, ya kuma bayyana fatansa na cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wajen karfafa sha’awar koyon sana’o’i tare da kulla alaka da cibiyar, a matsayin hanyar kawar da talauci.

Kazalika, ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da ma’aikatar ta fara ziyarar aiki a karkashin kulawar sa, yana mai cewa ziyarar ta biyo bayan tsare-tsarer da ma’aitar shirya domin cika burinta a wannan gwamnti na bunaksa tattalin arziki.

Ya kara da cewa gwamnati mai ci tana kishin Farfado da harkar sarrafa karafa kuma ya ba da tabbacin cewa MTI, Onitsha za ta samu kulawa sosai a karkashin jagorancin shugaba Tinubu.

Tun da farko, Shugaban cibiyar ta MTI, Onitsha, Mista Bode Fakuade, ya nemi gwamnati ta maida hanka a kan cibiyar ta hanyar kara samar da ababen more rayuwa tare da samar da kudade, yana mai cewa hakan zai taimaka matuka yin tasiri wajen samar da sanaoin hannu ga matasa wanda Kuma hakan zai magance matsalar zaman kashe wando.

Ministan ya kuma kai ziyara a kamfanin kera motoci na Innoson Motors, dake garin Nnewi, inda Shugaban kamfanin Mista Innocent Chukwuma ya tarbe shi.

Da yake jawabi Mista Innocent ya ce a shirye ya ke ya marawa yunkurin gwamnatin tarayya na sake fasalin fannin sarrafa karafa.

Ministan da mukarrabansa sun kuma kai ziyarar ban girma ga basaraken Obosi, Igwe Chidubem Iweka.

Har ila yau, ya kuma kai ziyara a fadar Mai Martaba Sarkin Onisha, Igwe Nnanyelugo Nnaemeka Alfred Ugochukwu Achebe, inda duka sarakunan gargiyar biyu suka bayyana goyansa bayansu tare da yin addoin fatan alheri ga ministan a kokarin samar da hadin kai da ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *