Take a fresh look at your lifestyle.

KOTUN ARGENTINA TA BA DA UMARNIN SAKIN MA’AIKATAN JIRGIN VENEZUELAN DA AKA TSARE

0 130

Kotun daukaka kara ta kasar Argentina da ke La Plata a lardin Buenos Aires ta amince ma’aikatan jirgin 12 daga cikin 19 na wani jirgin Venezuela da aka tsare a watan Yuni su bar Argentina.

 

Rahotanni sun ce kotun ta ba da izinin tafiyar ma’aikatan jirgin su 12 sannan ta umarci alkali da ya warware binciken da ake yi kan ma’aikatan cikin kwanaki 10.

 

Kamfanin Mahan Air na Iran ya sayar da jirgin Emtrasur dakon kaya ga Venezuela shekara guda da ta wuce, a cewar kamfanin jirgin na Iran.

 

Jirgin ya isa birnin Buenos Aires ne a farkon watan Yuni, bisa ga bayanan bin diddigin jirgin, tare da ma’aikatan jirgin na Venezuela da Iran.

 

Hukumomin Argentina sun tsare jirgin ne saboda zarginsa da alaka da ta’addanci da kuma bayyana dalilinsa na shiga kasar.

 

Karanta kuma: Ta’addanci: Argentina ta ba da umarnin kama jirgin Venezuela

 

Zuwan ta ya haifar da wani batu na diflomasiyya ga Argentina, wanda Amurka ta zargi da tallafawa kasashen da Amurka ta sanya wa takunkumi; Iran da Venezuela

 

Wata kotun Amurka ta bukaci Argentina da ta kwace jirgin a watan Agusta, wanda ta yi a mako mai zuwa. Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce umarnin kotu na da nufin “sace” jirgin.

 

Kama jirgin ya haifar da fushi a birnin Caracas daga magoya bayan jam’iyya mai mulki, wadanda suka yi maci don neman a sake shi.

 

Iran da Venezuela na da alaka ta kut-da-kut tare da sanya hannu kan shirin hadin gwiwa na tsawon shekaru 20 a watan Yuni.

 

Shugaban kasar Argentina mai barin gado Alberto Fernandez ya soki takunkumin da Amurka ta kakabawa birnin Caracas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *