Take a fresh look at your lifestyle.

Sojojin Isra’ila Sun Yi Ruwan Bama-bamai A Yankin Asibitocin Gaza

0 160

Isra’ila na ci gaba da kai munanan hare-hare a kusa da wasu asibitoci da ke arewacin zirin Gaza, jami’ai a yankin da aka yi wa kawanya, sun ce an sake katse duk wata hanyar sadarwa da intanet a yankin.

 

 

Shugabar ofishin yada labarai na gwamnatin Hamas Salama Maarouf ta ce, “Sama da sa’a guda, ana ta samun tashin bama-bamai a kusa da asibitoci.”

 

 

Makusancin babban asibitin Falasdinawa, Al Shifa, ya sha hare-hare na musamman a cewar Marouf.

 

 

Safwat Kahlout na gidan talabijin na Aljazeera, wanda ke bayar da rahoto daga Deir Al Balah a tsakiyar Gaza, ya kuma ce an kai hare-hare mafi muni a yankin da ke kewaye da asibitin.

 

 

“Za mu iya fahimtar cewa wadannan hare-hare ta sama na da nufin tura sojojin Isra’ila da ke kewaye da birnin Gaza zuwa asibitin Al Shifa. Mun san cewa dubban mutane sun bar gidajensu a wadannan unguwannin zuwa asibiti, suna neman mafaka,” inji shi.

 

 

“Wanda ke nuni da cewa Sojojin Isra’ila na shirin wani babban abu, watakila a cikin sa’o’i masu zuwa ko kuma a cikin kwanaki masu zuwa dangane da asibitin Al Shifa da kansa.”

 

 

Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata wani harin da Isra’ila ta kai a kusa da asibitin Al Quds da ke birnin Gaza, ya raunata akalla mutane 14 tare da lalata ginin.

 

 

Ƙungiya mai ba da shawara ta hanyar intanet ta ba da rahoton “katsewar Hanyar Sadarwa” a fadin Gaza. Kamfanin sadarwar Falasdinawa na Paltel ne ya tabbatar da katsewar.

 

 

Kakakin Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Juliette Touma ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa, “Mun rasa sadarwa tare da mafi yawan ‘yan tawagar UNRWA.”

 

 

An shafe sa’o’i 36 ne aka kafin a fara katsewar na zirin Gaza sannan na biyun na ‘yan sa’o’i kadan

 

Tommaso della Longa, mai magana da yawun kungiyar Red Cross da ke Geneva, ya ce “A asibitin mu na Al Quds, mun damu matuka game da lamarin saboda hare-haren da aka kai a kwanaki na karshe, a kusa da asibitin.” in ji Cross da Red Crescent.

 

An kai hari a asibitoci da motocin daukar marasa lafiya sau da yawa tun bayan fara kai hare-hare na baya bayan nan na Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe marasa lafiya, fararen hula da ke mafaka a wuraren da ma’aikatan lafiya.

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *