Kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC), ta ce an auna ayarin motocinta na manyan motoci biyar da motoci biyu dauke da kayayyakin kiwon lafiya na ceton rai a Gaza. Motoci biyu sun lalace sannan wani direba ya samu rauni.
Isra’ila na kashe yaran Falasdinawa da ba a taba yin irinsa ba, a cewar kungiyar kare hakkin yara, Defence for Children International-Palestine.
Akalla Falasdinawa 10,328 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.
A halin da ake ciki kuma, kasar Saudiyya za ta karbi bakuncin tarukan kasashen Larabawa, Afirka da kuma kasashen musulmi, domin tattauna rikicin Gaza a cikin kwanaki masu zuwa, in ji ministan zuba jari na kasar.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply