Darakta Janar na Muryar Najeriya (VON), Jibrin Ndace ya bayyana aniyar shi ta hada gwiwa da wata kungiyar yada labarai, PRNigeria domin cimma burin kungiyar.
Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a ofishin shi da wata tawaga karkashin jagorancin Malam Yushau Shuaib, Babban Editan Kamfanin PRNigeria daga Kamfanin IMPR masu buga PRNigeria.
Babban daraktan ya kuma yaba da kwarewar Shu’aib a fannin hulda da jama’a tare da bayyana dogaron da Shu’aib yake bayarwa da kuma goyon bayan VON.
Ndace wanda ya kuma karfafa gwiwar ma’aikatan IMPR da su ci gaba da sadaukar da kai ga ci gaban kungiyarsu, ya jaddada kudirin VON na hada kai da fitattun kungiyoyin yada labarai da kwararrun kungiyoyi, na gida da waje, domin cimma manufofin kungiyar.
A nashi jawabin, Malam Shuaib ya taya shi murnar nadin da aka yi masa a matsayin Darakta Janar na Muryar Najeriya, inda ya amince da shi a matsayin kwararren dan jarida wanda ya taka rawar gani a wannan fanni.
Shuaib ya bayyana imanin shi game da iya shugabancin Ndace kuma ya mika fatan alheri ga sabon mukamin shi.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply