Take a fresh look at your lifestyle.

Jihar Kwara Ta Ware Naira Miliyan 200 Domin Kawo Karshen Bayan Gida A Fili

2 106

Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana shirinta na hada kai da duk wata hukumar bada tallafi domin kawar da bahaya a fili a jihar. Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar Yunusa Lade, ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da wata kwararriyar hukumar wanke hannu ta asusun bada agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya Misis Theressa Pammer ta ziyarci ofishin shi dake Ilori babban birnin jihar.

 

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Kwara ta hada gwiwa da Unicef ​​domin kawo karshen bahaya a fili

 

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta ware naira miliyan 200 domin samar da bandakuna da sauran abubuwan da za su hana yin bayan gida a fili.

 

Ya ce ‘yan majalisar na matakin jiha da na tarayya sun dukufa wajen ganin sun kara kaimi a kokarin gwamnatin jihar na kawar da bayan gida a fili.

 

Tun da farko, kwararriyar wankin UNICEF daga ofishin Kaduna, Misis Theressa Pammer, ta shaida wa mahukuntan ma’aikatar cewa ta je jihar Kwara ne domin ganin yadda kungiyarta za ta tallafa wa jihar wajen kawar da bahaya a fili.

 

 

 

PUNCH/Ladan Nasidi.

2 responses to “Jihar Kwara Ta Ware Naira Miliyan 200 Domin Kawo Karshen Bayan Gida A Fili”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *