Take a fresh look at your lifestyle.

NASARAR AIKI: SHUGABA BUHARI YA YABA WA HUKUMAR NDLEA

0 273

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa ritaya murnar nasarar da hukumar ta samu a kwanakin baya.

 

Aikin ya kai ga nasara kama wata cibiyar hada magunguna ta kasa da kasa tare da kwato kilogiram 1,855 na hodar iblis.

 

A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban hukumar NDLEA daga birnin New York, inda yake halartar taron majalisar dinkin duniya karo na 77, UNGA 77, shugaba Buhari ya ce labarin samun sauki ya faranta ransa.

 

Ya ce: “Ina matukar godiya da aikin da kuka yi wajen kawar da barazanar muggan kwayoyi. Ya faranta min rai yayin da nake ci gaba da bin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin ku.

 

“Kun nuna sau da yawa cewa zabar da akayi muku  don jagorantar wannan yaƙin da miyagun ‘yan kasuwar haramtattun kwayoyi waɗanda kawai manufarsu ita ce lalata wa matasanmu rayuka da kuma dagula makomar matasanmu, zaɓi ne mai kyau. Da fatan za a ci gaba da aikin.

 

 A wata ganawa da ya yi da ‘yan tawagarsa , shugaban ya ce, “Buba Marwa yana cikin koshin lafiya.kamen Ton biyu na hodar iblis, kyakyawar nasara ce.

 

Hukumar NDLEA ta sanar da kama manyan dillalen hodar iblis da ta kai sama da dala miliyan 278 tare da kama manyan dillalen miyagun kwayoyi ciki har da wani dan kasar waje a wani babban samame da aka kwashe kwanaki biyu ana yi a wurare daban-daban a Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *