Hukumomin kasar Mexico sun sanar da cewa, an kashe mutane goma sha biyu a wani hari da aka kai a wurin wani biki a jihar Guanajuato da ke tsakiyar kasar Mexico.
An kai harin ne da asuba a garin Salvatierra lokacin da wata kungiya dauke da makamai suka bude wuta kan masu halartar bikin posada, bikin gargajiya na Mexico da aka gudanar a kwanaki kafin Kirsimeti, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.
Ofishin Babban Lauyan Jihar ya ce a kan X an kashe mutane 12 ba tare da yin karin bayani ba.
Guanajuato, gida ne ga dimbin masana’antun kera motoci da na jiragen sama, a shekarun baya-bayan nan ta zama daya daga cikin jihohin da suka fi fama da tashe-tashen hankula a kasar, yayin da ake gwabzawa tsakanin kungiyoyin masu safarar muggan kwayoyi.
REUTERS/Ladan Nasidi.