Take a fresh look at your lifestyle.

Tattaunawar Zaman Lafiya Tsakanin Afghanistan Da Pakistan Ya Ci Tura, Ko Da Ana Ci Gaba Da Tsagaita Wuta

10

Tattaunawar zaman lafiya tsakanin Afganistan da Pakistan ta wargaje, ko da yake ana ci gaba da tsagaita bude wuta tsakanin makwabtan kasashen kudancin Asiya, in ji kakakin Taliban.

Zabihullah Mujahid ya ce tattaunawar ta ci tura saboda dagewar da Islamabad ta yi na cewa Afganistan ta dauki alhakin tsaron cikin gida na Pakistan, bukatar da ya bayyana da ta wuce “karfin Afghanistan”.

Amma, ya ce, “Ayyukan tsagaita wuta da aka kafa ba mu karya ba har zuwa yanzu, kuma za a ci gaba da kiyaye shi.”

Zabihullah Mujahid ya ce tattaunawar ta ci tura saboda dagewar da Islamabad ta yi na cewa Afganistan ta dauki alhakin tsaron cikin gida na Pakistan, bukatar da ya bayyana da ta wuce “karfin Afghanistan”.

Amma, ya ce, “Ayyukan tsagaita wuta da aka kafa ba mu karya ba ya zuwa yanzu, kuma za a ci gaba da kiyaye shi.”

A ranar Juma’a ministan tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya ce tattaunawar sulhu da Afghanistan da aka yi a Istanbul da nufin hana sake barkewar rikicin kan iyaka ta ruguje, ya kara da cewa za a tsagaita bude wuta muddin ba a samu hare-hare daga kasar Afghanistan ba.

Sojojin Afganistan da Pakistan sun yi musayar wuta na dan takaitaccen lokaci a kan iyakarsu a ranar Alhamis, a wannan rana kuma aka ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a Istanbul.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gana da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a birnin Baku a ranar Asabar din da ta gabata, inda ya ce yana fatan tattaunawar za ta samar da sakamako mai dorewa, kuma Turkiyya za ta ci gaba da taka rawa a cewar wata sanarwa daga ofishinsa.

Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza fada a watan da ya gabata, inda suka kashe mutane da dama, a tashin hankalin mafi muni tun bayan da kungiyar Taliban ta koma kan karagar mulki a Afghanistan a shekarar 2021.

Bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a birnin Doha a watan Oktoba, amma tattaunawar ta biyu da aka yi a Istanbul a makon da ya gabata ta kare ba tare da cimma wata doguwar yarjejeniya ba, sakamakon rashin jituwar da aka samu kan kungiyoyin ‘yan ta’adda masu adawa da Pakistan da ke aiki a cikin Afghanistan.

Shekaru da dama, Pakistan da Taliban suna da dangantaka mai kyau, amma dangantakar ta tabarbare sosai a cikin ‘yan shekarun nan.

Rikicin na Oktoba ya biyo bayan hare-haren da jiragen saman Pakistan suka kai a farkon watan a Kabul a cikin wasu wurare da aka yi wa shugaban Taliban na Pakistan hari.

 

Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.