A karon farko shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya amince cewa an kama wasu ‘yan gwagwarmayar kasar Kenya biyu da suka bata a kasarsa tsawon makonni biyar.
A watan da ya gabata, shaidun gani da ido sun ba da rahoton ganin Bob Njagi da Nicholas Oyoo da wasu mutane sanye da rigar rufe fuska suka tilasta su shiga mota bayan wani taron siyasa inda suke goyon bayan jagoran ‘yan adawar Uganda Bobi Wine.
An tabbatar da labarin sakin su a ranar Asabar.
A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a yammacin ranar Asabar da ta gabata Museveni ya bayyana mutanen biyu a matsayin “kwararraru a cikin tarzoma” wadanda aka sanya su “a cikin firiji na wasu kwanaki.”
Magoya bayansa sun tarbi Mista Njagi da Mista Oyoo a babban filin jirgin sama da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya a ranar Asabar.
“Kwanaki talatin da takwas na sace mutane ba abu ne mai sauki ba, ba mu yi tunanin cewa za mu fito da rai ba saboda sojoji ne suka sace mu,” in ji Mista Njagi.
Ministan harkokin wajen Kenya Musalia Mudavadi ya ce sakin nasu ya biyo bayan ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Kenya da Uganda.
BBC/Aisha. Yahaya, Lagos