Jam’iyyar PDP ta shawarci ‘yan majalisar dokokinta 27 da suka koma jam’iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Ribas da su bar kujerun su domin gudanar da sabon zabe.
Mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Malam Umar Damagum ne ya bukaci hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja bayan taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa kan harkokin siyasa a Ribas.
Ya ce bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, ‘yan majalisar sun rasa kujerunsu.
Ya bayyana cewa zabi daya da masu sauya shekar ke da su shine su nemi sabon mukami da kuma sake tsayawa takara a dandalin jam’iyyun siyasar da suke so.
“Don kaucewa shakku, babu wata baraka a cikin jam’iyyar PDP a matakin kasa ko jiha don tabbatar da sauya shekar ‘yan majalisar PDP.
“Sun bar kujerunsu ne saboda wasu dalilai da aka san su kuma ba za su iya komawa majalisar ba tare da zabukan da aka saba yi ba kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 da dokar zabe (2022) ya tanada.
“Bugu da kari, kakakin majalisar dokokin jihar Ribas, Hon. Ehie Edison, ya ayyana kujerun mambobin da suka sauya sheka a hukumance a matsayin wadanda ba kowa ba ne kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
“Majalisar ta Ribas, kasancewar ta zama Functus Officio (wanda aikinsa ko ikonsa ya kare) kan lamarin ba za ta iya sake shigar da tsoffin ‘yan majalisar ba sai ta hanyar sabon zabe.
“Don a nanata, dokar zabe (2022) ta bayyana a fili ta yadda babu wata kotu da ke da hurumin hana INEC gudanar da zabe a duk inda kuma a duk lokacin da aka samu gurbi a kowace mazabar zabe,” in ji Damagum.
Ya yi kira ga INEC da ta sanya ranar da za a gudanar da sabon zabe a mazabun wadanda suka sauya sheka.
Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar da su kasance masu hadin kai da kuma jajircewa wajen kare dimokuradiyyar tsarin mulki da bin doka da oda.
Damagum ya lura cewa da yawa daga cikin mambobi sun yi wa PDP aiki a zaben 2023.
‘Yan majalisar su 27 sun koma APC ne a ranar 11 ga watan Disamba.
NAN/Ladan Nasidi.