Take a fresh look at your lifestyle.

Isra’ila Ta Kara Kai Hare-Hare A Zirin Gaza Gabanin Kuri’ar Tsaro

100

Dakarun Isra’ila sun yi nuni da cewa suna kara fadada hare-harensu na kasa tare da wani sabon farmaki a tsakiyar Gaza a yau Juma’a, yayin da ake sa ran kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’a kan wani kudiri na kara yawan taimakon jin kai domin dakile barazanar yunwa.

 

A yayin da ake fatan cimma nasara a tattaunawar da ake yi a wannan mako a Masar da nufin ganin Isra’ila da Hamas da ke fada da juna su amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta, an ba da rahoton hare-hare ta sama, da makaman atilari da fada a yankunan Falasdinawa.

 

Sojojin Isra’ila a ranar Juma’a sun umurci mazauna Al-Bureij da ke tsakiyar Gaza da su koma Kudu cikin gaggawa, lamarin da ke nuni da wani sabon salon harin da aka kai a kasa wanda tuni ya lalata arewacin Zirin da kuma yin kutse a kudancin kasar.

 

Sai dai kuma, adadin mutanen da suka mutu a lokacin yakin ramuwar gayya da sojojin Isra’ila ke yi ya janyo karin suka daga kasashen duniya, har ma daga kawayen Amurka.

 

A cikin sabon bayanin da ta yi kan wadanda suka jikkata, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 20,057 tare da raunata 53,320 a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga Oktoba.

 

“Bayan fiye da watanni biyu na yakin, hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kaiwa Gaza, ya mayar da arewacin zirin Gaza tulin tarkace,” in ji kungiyar agaji ta MSF a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X. “A asibitin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. matattu da wadanda suka jikkata na ci gaba da zuwa kusan kowace rana… Babu inda babu lafiya.”

 

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

Comments are closed.