Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Katsina Ya Kaddamar Da Kwamitin Yaki Da Cin Zarafin Yaya Mata Da Yara Kanana

Kamilu Lawal,Katsina.

211

Bikin kaddamar Da Kwamitin Ya Gudana Ne A Birnin Katsina, Fadar Gwamnatin Jihar

 

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da wani kwamitin masu ruwa da tsaki domin kawo karshen cin zarafin yaya mata da yara kanana a jihar

 

Kaddamarwar na nufin kankamar hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsakin domin tunkarar aiwatar da tanadin dokar da gwamnatin jihar ta sanyawa hannu  domin kare hakkin yara daga cin zarafin da ake masu kamar yadda yake a kundin kasa da kasa da  gwamnatin tarayya ke aiwatarwa

 

A lokacin da yake kaddamar da yan kwamitin, gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa matakin wani al’amari ne da gwamnatin jihar ta dauka da mahimmanci a kokarin da ake na magance cin zarafin yara tare da daukar kwararan matakai  ga duk wadanda aka samu da laifin cin zarafin bil’adama a fadin jihar

 

Gwamnan ya bukaci yan kwamitin da su hada kai a tsakanin su tare da duk wani mai ruwa da tsaki domin tunkarar matsalar cin zarafin bil’adama a cikin al’umma da nufin kawo karshenta

 

Yana mai cewa; “matsalar cin zarafin dan’adam babbar matsalace da bata da wane bisa wannan dalili kadai, ya kamata a taru waje guda domin kawo karshen ta a cikin al’umma”.

 

Gwamna Radda ya bukace su da su kafa Kananan kwamitoci a yankunan jihar domin  yaki da matsalar ya isa zuwa matakai na gaba

 

Kwamitin da gwamnan ya kaddamar yana kalkashin jagorancin ma’aikatar harkokin mata ta jihar a matsayin Jagora

 

Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Katsina, Honorabul Zainab Musa Musawa wadda ta bayyana irin kokarin da ma’aikatar tayi wajen raba wasu yara daga kalubalen cin zarafin rayuwarsu, ta jaddada aniyar kwamitin wajen cigaba da kare hakkin yara da duk wani bil’adama daga kalubalen cin zarafin rayuwarsa

 

Zainab Musawa wadda ta bayyana godiyarta bisa hadin kai da goyon bayan da take samu wajen gwamna Dikko Radda da Uwar gidansa ta kuma  bukaci cikakken hadin kai daga sauran masu ruwa da tsaki kamar jami’an tsaro da alkalai da sarakuna hadi da iyayen yara domin cimma kudurin da aka sanya a gaba

 

Mambobin kwamitin sun hada da ma’aikatar sharia da ta lafiya da watsa labarai hadi da hukumar wayar da kan al’umma ta kasa (NOA)

 

Kazalika ma’aikatar Kasafin kudin jihar da ofishin matar gwamna da sashen kula da ilmin yaya mata da SEMA hadi da babban alkalin jihar da hukumar kare hakkin dan adam ta kasa da jami’an tsaro na daga cikin membobin kwamitin

 

Sauran abokar huddar kwamitin sun hada da malaman addini da sarakunan gargajiya da kungiyoyin fararen hula da na agaji hadi da hukumomin kasa da kasa dake bada tallafi ga kananan yara da al’umma, kamar UNICEF da Save the children da IOM da AGILE da HILWA da dai sauransu.

 

 

Kamilu Lawal.

Comments are closed.