Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Taya Diyar Janar Murtala Murnar Cika Shekaru 60

217

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama diyar marigayi Janar Murtala Muhammed, Dr. Aisha Muhammed-Oyebode yayin da ta cika shekara 60.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya sanyawa hannu, shugaba Tinubu ya yabawa jajircewar Dr Muhammed Oyebode na tabbatar da adalci ga al’umma da kuma irin gagarumar gudunmawar da ta bayar a fannin shari’a, ayyukan jin kai, makarantu, da hidimar jama’a.

Da yake tunawa da misalan jagoranci na marigayi Janar Murtala Muhammed, shugaban kasar ya bayyana cewa Dr. A’isha diyar shugabar, ta kiyaye dabi’un ‘ya’yanta tare da tafiyar rayuwarta na kishi da juriya.

Yayin da yake yiwa Dr. Aisha fatan karin shekaru masu yawa a cikin koshin lafiya, shugaba Tinubu ya godewa babbar mai bayar da shawara kan sadaukar da kai ga yiwa Najeriya hidima.

 

Comments are closed.