Mallam Jibrin Baba Ndace, Darakta Janar na gidan rediyon Muryar Najeriya ya taya jami’an soji da aka yi wa karin girma da ritaya a rundunar sojojin Najeriya kwanan nan.
Da yake yaba wa Hafsoshin da suka yi ritaya bisa irin kyakkyawar hidimar da suke yi wa kasa, Mallam Ndace ya yi kira ga sabbin jami’an da aka kara musu girma da su ga girman su a matsayin wata dama ta ba da gudunmowar su wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan Sojoji na kare martabar yankunan kasa da kuma tabbatar da aminci ga al’umma da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.
Daga nan sai DG din ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da mara wa kokarin sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro wajen magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasar.
Mallam Jibrin Baba Ndace ya kara nanata kudurin Muryar Najeriya karkashin jagorancin shi na ci gaba da inganta hadin gwiwa da ake yi da sojoji da sauran Hukumomin tsaro wajen fito da kyawawan martabar Najeriya a duniya.
Wani bincike da aka yi kan manyan hafsoshin da aka yi wa karin girma ya nuna cewa an yi wa jimillar manyan hafsoshi 217 karin girma a sassan Sojoji da na ruwa da na sama. Da sojin kasa ke da kaso mafi yawa na 122, yayin da sojojin ruwa na Najeriya ke da 58 sannan sojojin sama na da manyan hafsoshi 37 da suka samu karin girma.
Haka kuma, jimillar Janar 113 da suka yi ritaya daga aikin soja, da suka hada da Janar daya, Laftanar Janar daya, Manjo Janar 67, da Birgediya Janar 44, wanda hakan ya kawo karshen ayyukan da suke yi a rundunar sojojin Nijeriya.
Ladan Nasidi.