Take a fresh look at your lifestyle.

Kwararre Ya Shawarci ‘Yan Najeriya Da Su Kula Da Lafiyar kwakwalwa

139

Daraktan kula da lafiya na asibitin masu tabin hankali na tarayya da ke Yaba a Legas, Dokta Olugbenga Owoeye, ya shawarci ‘yan Najeriya da su kula da lafiyar kwakwalwar su, inda ya ce idan har ta lalace, sai an yi kokairi sosai wajen gyara ta.

 

KU KARANTA KUMA: Asibitin masu tabin hankali a Legas ya samu karuwar karbar mutane dari bisa dari, in ji CMD

 

Ya bayar da shawarar ne a lokacin da shugaban kungiyar Rotary Club na Onigbongbo, Rasaq Babatunde Salau da sauran ‘yan kungiyar suka ziyarci asibitin domin taya majinyata murnar bikin Kirsimeti da kuma bayar da gudummawar kayayyaki da dama, wadanda suka hada da kayan tsafta, matashin tada kai da abubuwan amfani, da sauransu.

 

Owoeye ya ce abubuwan da ke haifar da tabin hankali sun hada da masu juna biyu da suka kamu da cutar, rauni, rashin abinci mai gina jiki, da rashin samun kulawar da ta dace da mata masu juna biyu da dai sauransu.

 

Sai dai ya yi gargadin cewa cututtuka kamar su ciwon sukari, hawan jini, ciwon daji, da dai sauransu, na iya janyo tabin hankali.

 

Salau ya ce, kungiyar mai kimanin shekaru 41, tana da al’adar ziyartar asibiti tun a shekarar 1984 domin yin bikin Kirsimeti tare da su da kuma ba da kyaututtuka.

 

Ya ce, “A bana, mun ziyarci  Unguwanni Mata, Cibiyar kula da Mahaukata, Ma’aikatar Tsofaffi da Kula da masu tabin hankali domin ba marasa lafiya kyaututtuka, mun karrama su da taya su murnar Kirsimeti.

 

“Ya kamata ‘yan Najeriya su ba da muhimmanci a cikin jigon bikin Kirsimeti, wanda ke ba wa talakawa tallafi yayin da ya kamata gwamnati ta kara kaimi wajen kula da marasa galihu.”

 

Har ila yau, Kungiyar Ladies Helpers Union, Cocin Cathedral Church of Christ, karkashin jagorancin tsohon shugaban ta, Modupe Alesinloye Williams, da kungiyar abokan asibiti, karkashin jagorancin sakataren ta, Lanre Akeredolu, sun ziyarci asibitin domin dubiya ga marasa lafiya da kuma bayar da gudummawar talabijin na plasma da sauran kyaututtuka.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.