Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Yi Makokin Tsohon Kakakin Majalisa, Na’Abba

136

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana bakin cikin shi kan rasuwar tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na’Abba, CFR.

 

 

 

Da yake jajantawa iyalan Na’ Abba, gwamnati, da al’ummar Jihar Kano, Shugaban ya nuna alhininsa kan rashin, tare da tunawa da irin gudunmawar da marigayi tsohon dan majalisar ya bayar wajen gina kasa ta hanyar doka, shawarwari, da manufofi.

 

 

 

Shugaba Tinubu a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya tuno da gwagwarmayar da kakakin majalisar Na’Abba ya yi wajen kare ayyuka da rawar da majalisa ke takawa a harkokin mulki.

 

 

 

Shugaban na Najeriya ya bayyana tsohon dan majalisar a matsayin dan siyasa mai da’a da jajircewa.

 

 

 

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma yi wa wadanda suka yi jimamin rashin lafiya ta’aziyya.

 

 

 

Marigayi Na’Abba shi ne kakakin majalisar wakilai bayan dawowar mulkin dimokradiyya a Najeriya daga 1999 zuwa 2003, ya gaji Salisu Buhari.

 

 

 

An haifi Ghali Umar Na’Abba a ranar 27 ga Satumba, 1958 kuma ya rasu a ranar 27 ga Disamba, 2023.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.