Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da wani gagarumin yunkuri na ganin Najeriya ta samu wadatuwa a fannin albarkatun man fetur a shekarar 2024, ta hanyar yunkurinta na sake fara tace kayayyakin cikin gida da matatar Fatakwal, da kuma matatar Dangote.
KU KARANTA KUMA: Na kuduri aniyar gina Najeriya mai adalci – Shugaba Tinubu
Shugaban ya ce a farkon shekarar 2024 matatun man za su fara aiki sosai.
Ya bayyana hakan ne yayin sakonsa na sabuwar shekara ga ‘yan Najeriya a ranar 1 ga watan Junairu, 2024.
Shugaban na Najeriya ya kuma bayyana cewa, a yanzu gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin kara kaimi wajen samar da ayyukan yi a sassa daban-daban bayan da ta aza harsashin tsare-tsaren farfado da tattalin arzikin Najeriya a cikin watanni bakwai da suka gabata.
Ya kuma jaddada aniyar shi na yin wata sabuwar yarjejeniyar samar da wutar lantarki domin kara samar da aikin samar da wutar lantarki ta Siemens Energy wanda ya ce za ta isar da ingantaccen wutar lantarki ga gidaje da kasuwannin Najeriya a karkashin shirin shugaban kasa na samar da wutar lantarki da aka fara a shekarar 2018.
KU KARANTA KUMA: Cikakken Jawabi: Jawabin Shugaban Najeriya Na Sabuwar Shekara
Shugaban ya kara da cewa sauran ayyukan samar da wutar lantarki da za su karfafa amincin layukan sadarwa da inganta hanyoyin sadarwa na kasa suna ci gaba da gudana a fadin kasar.
“Bayan kafa harsashin tsare-tsaren farfado da tattalin arzikin mu a cikin watanni bakwai da suka gabata na shekarar 2023, yanzu mun shirya tsaf domin kara saurin isar da hidimar mu a sassa daban-daban.
“A cikin watan Disamban da ya gabata yayin COP28 a Dubai, ni da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, mun amince kuma mun himmatu ga wata sabuwar yarjejeniya don hanzarta isar da aikin samar da wutar lantarki na Siemens wanda a ƙarshe zai isar da ingantaccen wutar lantarki ga gidajenmu da kasuwancinmu. Karkashin shirin samar da wutar lantarki na shugaban kasa wanda aka fara a shekarar 2018.
“Gwamnatina ta fahimci cewa babu wani sauyi mai ma’ana na tattalin arziki da zai iya faruwa ba tare da tsayayyen wutar lantarki ba. A shekarar 2024, muna ci gaba yunkurin mu na sake fara tace man fetur a cikin gida tare da matatar Fatakwal, da matatar Dangote wadda za ta fara aiki sosai.” In ji Shugaban.
Ladan Nasidi.