Take a fresh look at your lifestyle.

Jihar Legas Ta Amince Da Kyauta Ga Maaikatan LAWMA

121

Gwamnan jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya, Babajide Sanwo-Olu, ya amince da kyautar kudi na karshen shekara ga masu shara a titunan Legas, LAWMA.

 

Manajan Darakta/Shugaba na LAWMA, Dr. Muyiwa Gbadegesin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Legas, ya ce yana godiya ga muhimmiyar rawar da suke takawa na tsaftace Legas.

 

Gbadegesin ya ce jarumai masu himma da kwazo a harkar shara a Legas sun yaba da wannan karamcin da gwamnan ya yi.

 

“Gov. Sanwo-Olu ya amince da namijin kokarin da masu shara a titunan mu ke yi wajen kiyaye tsabta da lafiya ga al’ummar Legas.

 

“Wannan kyautar wata alama ce ta nuna godiya ga sadaukarwar da suka yi, musamman a wannan lokacin bukukuwa,” in ji shi.

 

Gbadegesin ya ce, wannan garabasar za ta yi tasiri ga rayuwar wadanda aka karbo da kuma iyalansu, wanda zai kawo farin ciki da annashuwa a wannan kakar.

 

Ya ce labarin ya samu ‘yar murna a tsakanin ma’aikatan tsaftar muhalli, saboda sun nuna jin dadin su da wannan karamcin da gwamnan ya yi.

 

Shugaban na LAWMA wanda ya yi wa mazauna yankin murnar shiga sabuwar shekara, ya kuma ba da tabbacin hukumar za ta ci gaba da bayar da hadin kai a kan kokarin da take yi na tabbatar da tsaftar dukkan sassan jihar a shekarar 2024.

 

Sanwo-Olu ya kuma amince da kara wa duk ma’aikatan jihar kyauta na karshen shekara saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da jihar gaba.

 

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

Comments are closed.