Koriya ta Arewa ta harba makaman atilare sama da 200 a gabar tekun yammacin ta, zuwa tsibirin Yeonpyeong na Kudu, in ji rundunar sojin Seoul.
Nan da nan Koriya ta Kudu ta ba da sanarwar ficewa ga fararen hula a tsibirin, amma har yanzu ba ta tabbatar da ko tana da alaka da harin ba.
Kudancin kasar dai ya yi Allah-wadai da matakin, inda suka kira shi a matsayin “aiki ne na tunzura jama’a”.
A shekara ta 2010, makaman roka na Koriya ta Arewa sun yi luguden wuta da dama a tsibirin Yeonpyeong, inda suka kashe mutane hudu.
Harsashin makaman da aka harba a ranar Juma’a da misalin karfe 09:00 zuwa 11:00 agogon kasar (00:00 zuwa 02:00 agogon GMT) ba su shiga yankin Koriya ta Kudu ba yayin da dukkansu suka sauka a yankin da ke tsakanin kasashen biyu.
Hafsan hafsoshin sojojin Koriya ta Kudu sun ce lamarin bai haifar da “lalata ga jama’armu ko sojojinmu ba”, amma ya kara da cewa matakin “yana barazana ga zaman lafiya a zirin Koriya da kuma tayar da hankali”.
Harin dai ya biyo bayan gargadin da Pyongyang ta yi na cewa tana gina makamanta na soji a shirye-shiryen yakin da ka iya ” barke a kowane lokaci” a gabar tekun.
Hukumomin tsibirin Baengnyeong da ke kusa da su kuma sun ba da rahoton umarnin kwashe mutanen a can.
Wannan lamari na baya-bayan nan ya zo ne watanni bayan da Koriya ta Arewa ta dakatar da yarjejeniyar soji da ta kulla da Kudancin kasar da nufin kyautata alaka.
Bayan haka, Pyongyang ta ce za ta janye dukkan matakan “dauka don hana rikicin soji a dukkan bangarori da suka hada da kasa, ruwa da iska”, tare da tura “kwararrun sojoji da sabbin kayan aikin soja” a yankin kan iyaka.
Duk da haka, Koriya ta Arewa ta saba wa yarjejeniyar sau da yawa a cikin shekaru biyu da suka gabata, ta harba makamai masu linzami da kuma harba manyan bindigogi a cikin tekun ta hanyar Kudu. A karo na karshe da Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami a cikin tekun shi ne a watan Disambar 2022, inda a cikin wannan shekarar kadai aka samu irin wadannan abubuwa guda tara.
Tsibirin Yeonpyeong, gida ne ga sansanin soji da kuma fararen hula kusan mutane 2,000, yana tazarar kilomita 3 (mil 2) daga kan iyakar teku da ake takaddama a kai a Tekun Yellow da kuma kilomita 12 daga gabar tekun Koriya ta Arewa.
An shafe shekaru ana gwabza fada tsakanin sojojin ruwan Koriya ta Arewa.
A shekara ta 2010, an kashe sojoji biyu da farar hula biyu bayan da Koriya ta Arewa ta harba makaman atilare da dama zuwa tsibirin.
BBC/Ladan Nasidi.