Ministan tsaron Isra’ila ya ce za a ci gaba da kai hare-hare a Kudancin Gaza, wadanda suka hada da harin bama-bamai kan sansanonin ‘yan gudun hijira da a baya ta ayyana ‘yankunan tsaro’ na farar hula.
Akalla mutane 32 aka kashe a Khan Younis da biyar a Rafah yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce mutane 125 ne suka mutu yayin da 318 suka jikkata a cikin sa’o’i 24.
Akalla mutane 22,438 ne suka mutu yayin da wasu 57,614 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba. Yawan wadanda suka mutu sakamakon harin da aka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 1,139.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.