Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Ta Fidda Jerin Karshe Na Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Na Afirka

107

Gabanin wasan neman gurbin shiga gasar kwallon ragar na Afirka, babban mai horar da ‘yan wasan mata na Najeriya Samuel Ajayi ya bayyana sunayen ‘yan wasa 12 da za su wakilci kasar.

 

KU KARANTA KUMA: Masar ta doke Najeriya a gasar kwallon ragar ‘yan mata ta ‘yan kasa da shekaru 17

 

Tun a karshen watan Disamba ne kungiyar da ke karkashin koci Ajayi ta kasance a cikin wani sansani a rufe, kuma kungiyar ta kasa rage ‘yan wasa 12 bayan da ta yi atisaye.

 

‘Yan wasa biyar daga ‘yan kasa da shekara 21 da biyu daga ‘yan kasa da shekaru 17 ne suka yi kungiyar yayin da Ijeoma Ukpabi Jummai da Bitrus za su kasance kyaftin da mataimakin kyaftin din kungiyar.

 

A ranar 4 zuwa 8 ga watan Janairu ne ake sa ran za a gudanar da wasannin share fage na gasar kwallon volleyball na Afirka karo na 13 a babban filin wasa na kasa da ke Legas.

 

Jerin Karshe

 

Ijeoma Ukpabi (Captain), Sharon Achi, Aliyah Usman, Maryam Ibrahim, Mirabel Onyegwu, Happy Wushilang, Blessing Unekwe, Deborah Chukwu, Ifunanya Udeagbala, Kelechi Ndukauba, Albertina Francis da Jummai Bitrus.

Babban kocin shine Samuel Ajayi yayin da Ezechukwu Oguamalam shine mataimakin koci.

 

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.