Take a fresh look at your lifestyle.

CAF Ta Kara Lambar Yabo Ta AFCON Da Kashi 40%

104

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da karin kashi 40 cikin 100 na kyautar Kudi ga wanda ya lashe gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta AFCON a kasar Cote d’Ivoire 2023.

 

Wanda ya ci nasarar TotalEnergies AFCON Cote d’Ivoire 2023 zai sami dalar Amurka 7 000 000.

 

KU KARANTA KUMA: 2023 AFCO: Super Eagles za ta kara da kungiyoyin Afrika biyu

 

Wanda ya zo na biyu na TotalEnergies AFCON Cote d’Ivoire 2023 a yanzu zai sami dalar Amurka 4 000 000. Kowanne daga cikin ‘yan wasan Semi-final guda biyu zai sami USD 2 500 000 kuma kowane na hudu na Quarter-final, USD 1 300 000.

 

Shugaban hukumar ta CAF Dr Patrice Motsepe ya ce: “CAF ta samu ci gaba sosai a cikin shekaru biyu da suka gabata wajen kara samun kyautar kudin AFCON da duk sauran manyan gasa. Mun kara kudin kyautar dan wasan AFCON zuwa dalar Amurka 7 000 000 wanda hakan ya karu da kashi 40 cikin 100 idan aka kwatanta da kudin da aka samu na AFCON a baya. Ina da yakinin cewa wani kaso na Kudi na Kyautar zai taimaka wajen bunkasa harkar kwallon kafa da kuma amfanar da duk masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa, tare da taimaka wa Kungiyoyin Mambobin mu da gwamnatocin su”.

 

 

CAF/Ladan Nasidi.

Comments are closed.