Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce ba dole ba ne a tursasa Falasdinawa su fice daga Gaza, kuma dole ne a bar su su koma gidajensu da zarar sharudda suka bayar.
Blinken yayi Allah wadai da kalaman wasu Ministocin Isra’ila, wadanda suka yi kira da a sake tsugunar da Falasdinawa a wasu wurare.
Jami’in na Amurka ya je Qatar ne a ziyarar shi ta baya-bayan nan a Gabas ta Tsakiya.
Kalaman nasa sun biyo bayan rahotannin da ke cewa an kashe mutane kusan 70 a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza.
Hotunan Jabalia sun nuna gawarwaki kwance a cikin baraguzan ginin da aka lalata – yawancinsu mata da yara.
Fiye da Falasdinawa 60 kuma an ba da rahoton an kashe su a ranar da ta gabata a birnin Khan Younis na Kudancin kasar.
An sha kai hare-hare a sansanin Jabalia tun lokacin da Isra’ila ta fara yakin da Hamas bayan harin da ‘yan bindigar Hamas suka kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
Fiye da mutane 22,000 akasari mata da yara – aka kashe a Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas. An ba da rahoton mutuwar mutane 113 a cikin sa’o’i 24 na harin bam na Isra’ila.
BBC/ Ladan Nasidi.