Tsohuwar ministar harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma ta Najeriya, Sadiya Umar-Farouq, ta isa hedikwatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, domin amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi mata.
Gayyatar ita ce bayar da ƙarin haske game da wasu batutuwan kuɗi da Hukumar ke bincike.
A wata sanarwa da tsohuwar mai baiwa ministar shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Nneka Anibeze ta fitar, tsohuwar ministar ta nuna a shirye ta ke ta karrama gayyatar da hukumar ta yi mata.
“Na ci gaba da alfahari da cewa na yi wa kasata hidima a matsayina na ministar Tarayyar Najeriya da kowane irin nauyi, kuma zan kare ayyukana, gudanar da ayyuka da kuma shirye-shirye a lokacin da nake mulki a duk lokacin da aka kira ni da yin hakan,” in ji ta.
Ta kai Ziyarar ce ga ofishin EFCC da ke gundumar Jabi a Abuja a ranar Litinin.
Ladan Nasidi.