Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Tallafawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Daminar Da Ta Gabata

Kamilu Lawal,Katsina.

243

Gwamnatin jihar Katsina ta kafa kwamiti domin tallafawa wadanda suka gamu da ibtila’in ambaliyar ruwa a daminar da ta gabata ya tallafa wa kashi na biyu na wadanda lamarin ya shafa a jihar.

 

Kayayyakin tallafin da kwamitin ya rarraba wa wadanda lamarin ya shafa a kananan hukumomi takwas dake jihar sun hada da siminti da kwanon rufi  da ‘kusa hadi da turamen zannuwa domin sutura ga mata.

 

Da yake jawabi a wajen kaddamar da Rabon a karamar hukumar Katsina, shugaban kwamitin da gwamnatin ta kafa domin rarraba kayan, babban sakatare a gidan gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Yusuf Nasir ya bayyana cewa gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda ne ya bada umarnin rabawa wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a daminar da ta gabata.

 

Yace tallafin na da nufin ragewa wadanda lamarin ya shafa radadin abinda ya same su, yana mai bayyana ibtila’in a matsayin wata kaddara da Allah ya jarabce su da ita inda ya bukace su dasu maida lamurran su zuwa ga Allah domin samun ikon cin jarabawar da ya dora masu.

 

Daga nan sai ya bukaci wadanda suka samu tallafin da suyi amfani da kayan yadda ya kamata, Yana mai jaddada kudurin kwamitin na tabbatar da tallafin ya isa ga dukkanin wadanda suka cancanta a fadin jihar domin tabbatar da cikar muradin gwamnan jihar, Malam Dikko Radda na ganin ya tallafawa masu karamin karfi da mabukata a fadin jihar.

A nata jawabin a wajen taron, shugabar hukumar bada agajin gaggawa (SEMA) ta jihar Katsina, Hajiya Binta Hussaini Dangani ta bada tabbacin hukumar na cigaba da tallafawa wadanda lamarin ambaliyar ya shafa domin tabbatar da an ragewa dukkanin wadanda lamarin ya shafa radadin abinda ya same su.

 

Tace a kashi na biyun wanda aka kaddamar an tanadi kayayyakin ne domin rabawa ga  mutane sama da dari hudu (400) wadanda lamarin ya shafa bayan wasu mutane sun amfana a kashin farko da aka gudanar a watannin da suka gabata.

 

Wadanda suka amfana da tallafin cike da farin ciki da murna a fuskokin su sun godema gwamnan jihar  Katsina, Malam Dikko Radda bisa samar masu da tallafin, suna masu yi masa fatan Alheri tare da fatan samun nasarar cimma kudurorinsa na ciyar da jihar Katsina gaba.

 

Kazalika sun yabama yan kwamitin bisa yadda suka tabbatar da cewa tallafin ya kawo garesu tare da bada tabbacin cewa zasu yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata.

 

Kamilu Lawal.

 

Comments are closed.