Take a fresh look at your lifestyle.

Zaftarewar kasa Ya kashe Mutane 22 A Tanzaniya

99

Mutane 22 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a wata mahakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a arewacin Tanzaniya, in ji jami’ai.

 

Lamarin ya faru ne a ma’adanin Ng’alita da ke gundumar Bariadi, a yankin Simiyu ranar Asabar, in ji kwamishinan gundumar Simon Simalenga.

 

Hakan ya faru ne bayan da wasu gungun mutane suka fara aikin hakar ma’adinai a wani yanki da aka takaita ayyukan saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

 

Shugaba Samia Suluhu Hassan ta bayyana “bakin ciki” da wannan labari.

 

“Wadannan ƴan ƙasar Tanzaniya ƙanana ne masu hakar ma’adinai a yankin, suna ƙoƙarin samun abin dogaro da kansu, da iyalansu,” in ji ta a cikin wani rubutu a kan X, wanda aka fi sani da Twitter.

 

Mista Simalenga ya ce da farko an gaya masa cewa akwai mutane 19 zuwa 20 da suka makale a cikin mahakar ma’adinan, amma gawarwaki 22 ya kare.

 

Mukaddashin kwamandan hukumar kashe gobara da ceto na yankin Faustine Mtitu, ya ce a cikin alkalumman da kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar na cewa, an kawo karshen binciken ne saboda yana da tabbacin cewa babu sauran gawarwakin da suka makale a cikin baraguzan ginin.

 

Mista Simalenga ya ce gungun mutanen sun fara aikin hakar ma’adinai a yankin mai arzikin ma’adinai kimanin makonni uku da suka wuce kafin gwamnati ta kawo matakan kare lafiyarsu.

 

An takaita yankin ne saboda ruwan sama da ake ci gaba da yi, wanda ya haddasa ambaliyar ruwa.

 

“Jami’in hakar ma’adinai na yankin ya ziyarce su kuma ya hana su aikin hakar ma’adinai yayin da suke aiki kan hanyoyin da ake bukata” in ji Mista Simalenga.

 

Ana yin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida a Tanzaniya, wacce ke daya daga cikin manyan masu samar da zinare a duniya.

 

BBC/Ladan Nasidi.

Comments are closed.