An rufe makarantu a kasar Mauritius a daidai lokacin da ake hasashen za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da zai haifar da ambaliya.
Tsibirin Réunion na Faransa da ke kusa da shi a ranar Litinin ya kasance a kan matakin faɗakarwa mafi girma bayan da guguwar Belal ta afka Wa Tsibirin.
Hukumomin kasar sun gargadi mazauna garin da su kasance a cikin gida sannan kuma ba a ba wa jami’an agaji damar shiga tsakani ba.
Matsanancin yanayi ya haifar da asarar rayuka a cikin Réunion da Mauritius.
An gano gawar wani magidanci a ƙauye wurin shakatawa na Saint-Gilles da ke yammacin gabar tekun Réunion jim kaɗan kafin a ɗaukaka faɗakarwar guguwar daga ja zuwa wani launi ranar Litinin.
Hukumomi sun ce mutumin ya ki a ceto shi.
A kauyen Baie-du-Tombeau na Mauritius, wani dattijo mai shekaru 75 ya nutse a ruwa ranar Lahadi.
Masu hawan igiyar ruwa biyu sun fuskanci guguwar a tekun La Preneuse da ke yammacin Mauritius. Ɗayan ya isa gaɓar teku, yayin da ɗayan kuma ya ɓace.
BBC/Ladan Nasidi.