Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Jagoranci Bikin Tunawa Da Sojojin Kasar

99

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya jagoranci shugabannin majalisar kasa, da sojoji da sauran masu ruwa da tsaki wajen karrama jaruman da suka mutu a kabarin soja Dogon Yaro,  a Abuja.

 

Bikin ya kasance karshen ayyukan da aka fara da kaddamar da Tambarin tunawa da Sojojin kasar a watan Oktoban da ya gabata.

 

Wadanda suka shaida taron sun hada da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas; Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, Alkalin Alkalan Tarayya; Olukayode Ariwoola; da sauransu.

 

An gudanar da addu’o’in kiristoci da musulmi domin samun kwanciyar hankali ga rayukan jaruman da suka rasu sannan aka yi shiru na minti daya.

 

Shugaba Tinubu ne ya jagoranci bikin shimfida furannin a kasan kabarin Dogon Yaro.

Wannan shi ne karon farko da shugaban kasar ya aza furen ga AFRD.

 

Daga nan sai Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai, CJN, Ministan Babban Birnin Tarayya, Karamin Ministan Tsaro da Doyen na Diflomasiyya a Najeriya.

 

Shugabannin hafsoshin da Sufeto Janar na ‘yan sanda da dai sauransu sun yi nasu ban girna wajen shimfida furanni.

 

Sojoji dauke da makamai ne suka yi ta harbin sama wajen biki a wani bangare na al’adar zagayowar wannan bukukuwan sojoji.

 

Daga nan ne kuma shugaba Tinubu ya rattaba hannu a kan rajistar bikin tunawa da sojojin kasar kafin ya saki fararen tantabaru.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.