Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai halarci bikin rantsar da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma karo na biyu, wanda nan da sa’o’i kadan na ranar Litinin 15 ga watan Janairu, za a fara a filin wasa na Dan Anyiam, Owerri babban birnin jihar.
Kafin halartar bikin, shugaban zai kaddamar da titin filin jirgin sama da aka yi wa gyaran fuska wanda a halin yanzu aka mayar da shi daga hanyoyi biyu zuwa hanyoyi hudu tare da fitulun gefe daga titin Owerri-Aba zuwa filin jirgin sama har da sabbin tagwayen kofofin shiga.
Shugaban kasar zai samu rakiyar wasu jami’ai da ‘yan majalisar dokokin kasar wadanda kuma za su halarci kaddamar da wasu ayyuka a jihar.
Shugabannin jam’iyyar na jam’iyyar All Progressives Congress, mambobin kungiyar gwamnonin ci gaba da kuma wasu mambobin majalisar ministocin shugaba Tinubu za su halarci bikin rantsarwar.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Gwamna Uzodimma a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 11 ga watan Nuwamba, bayan nasarar da ya samu a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar Imo.
Jihar na cikin wani yanayi na biki, kuma babban birnin Owerri na shirin karbar manyan baki .
An samar da isassun matakan tsaro, kuma an dauki matakan da suka dace domin kula da jama’ar da ake sa ran zuwan su.
Ladan Nasidi.