Take a fresh look at your lifestyle.

Al’ummar Mali Sun Yi Zanga-Zangar Adawa Da Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Na Majalisar Dinkin Duniya

114

Masu zanga-zangar dai sun daga tutocin kasar Mali tare da rera taken kin jinin MDD.

 

Wasu kuma na dauke da tutocin kasar Rasha yayin da suke tafiya cikin titunan babban birnin kasar.

 

Gwamnatin sojin Mali ta yi tsami tsakaninta da tawagar Majalisar Dinkin Duniya da aka fi sani da MINUSMA, inda a watan Yuli ake tsare da sojojin Ivory Coast bayan ta bayyana su a matsayin sojojin haya.

 

“MINUSMA ba ta yi komai ba a nan. Muna son su tafi. Mun zo nan don nuna wa al’ummar duniya cewa ba ma son MINUSMA. Ba mu damu da MINUSMA ba. Muna son kasarmu. Muna son sojojinmu karkashin jagorancin Kanar Assimi Goita,” in ji Lassina Doumbia, wani mai zanga-zangar.

 

” Za su iya komawa gidajensu su zauna a can. Ba ma buƙatar taimakonsu kuma. Assimi Goita ya ishe mu. Matasan Mali sun ishe mu,” in ji Samba M. Wangara.

 

Masu zanga-zangar dai sun zargi aikin da zagon kasa ga ‘yancin kasar ta Mali.

 

A cikin watan Yuli, hukumomin Mali sun dakatar da aikin karba-karba na dakarun wanzar da zaman lafiya kafin su janye shawarar bayan wata guda.

 

Dakarun mai karfi 12,000 sun kasance a kasar dake yammacin Afirka tun daga shekarar 2013.

 

labaran africa

Comments are closed.