Jami’ar Legas UNILAG da Jami’ar Jihar Legas LASU suka hada gwiwa wajen shirya karbar bakuncin gasar wasannin jami’o’in Afirka karo na 11, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 20 zuwa 29 ga Satumba, 2024.
Ƙungiyar wasanni ta Jami’ar Afirka ce ta shirya kuma an fara gudanar da shi a 1975 a Accra, Ghana.
Najeriya ta karbi bakuncin gasar a shekarar 2004 a jihar Bauchi, inda kasashe 15 suka fafata.
KU KARANTA KUMA: Gasar WAUG: Jami’ar Ghana ta lashe kofi na gasar a shekarar 2023
An fara sanar da UNILAG da LASU a matsayin masu karbar bakuncin gasar ta 10 da jami’ar Kenyatta ta Kenya ta dauki nauyin shiryawa a shekarar 2022. Kungiyar wasannin jami’o’in Najeriya ta hannun mukaddashin babban sakatarenta, Chidiebere Ezeani, ta tabbatar da hakan a ranar Alhamis a wata sanarwar manema labarai.
“Jami’ar Jihar Legas LASU da Jami’ar Legas UNILAG sun hada karfi da karfe a matsayin masu daukar nauyin wannan gagarumin taron, inda suka nuna himma wajen bunkasa wasannin motsa jiki a cikin al’ummar jami’ar Afirka,” in ji Ezeani.
“Babban abin tarihi na wannan taron shi ne hadin gwiwar mataimakan shugabannin jami’o’i mata. Farfesa Folasade Ogunsola, mataimakiyar shugabar jami’ar Legas ta 13, da takwararta, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello, mataimakin shugabar jami’ar jihar Legas na tara, za su jagoranci wannan gagarumin hadin gwiwa,” in ji sanarwar.
A cewar Ezeani, taron zai kunshi darussa da dama a tsakanin daidaikun mutane da kuma wasannin kungiya da suka hada da; wasannin, badminton, dara, Kokawa, kwallon kwando, ƙwallon ƙafa, da ƙwallon hannu.
FASU ta kuma ce za a kara yawan jami’o’i a gasar a bana, inda ake sa ran ‘yan wasa kusan 5000 za su shiga gasar.
A farkon wannan wata a yayin kaddamar da ayyuka a jami’ar jihar Legas a farkon wannan wata, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya jaddada kudirinsa na tallafawa kungiyoyin wasanni na jami’o’in Afrika.
Mataimakiyar shugabar kungiyar ta UNILAG, Farfesa Folasade Ogunsola ita ma ta bayyana shirinsu na karbar bakuncin nahiyar a kwanakin baya da suka karbi bakuncin wasannin NUGA.
“Za mu yi amfani da kyawawan wuraren da aka gyara lokacin da aka gudanar da Wasannin NUGA a cikin shekara ta 2021.”
Ta bayyana shirin inganta cibiyar wasanni ta jami’ar, ciki har da dakin kwanan dalibai mai gadaje 240 da aka kaddamar.
Shi ma takwararta ta LASU, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello ta bayyana muhimmancin wannan taron ga jihar Legas da sauran al’ummar jami’o’in Najeriya.
Mukaddashin shugaban kungiyar ta NUGA, Dokta Bawa Mohammed, ya yaba wa kungiyoyin da suka dauki nauyin gudanar da ayyukan su bisa ci gaba da bayar da gudunmawar su wajen bunkasa wasannin jami’o’i a Najeriya.
Ladan Nasidi.