Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya kaddamar da wani katafaren haikali ga gunkin Hindu Ram a birnin Ayodhya.
Wajen bautar ya maye gurbin wani masallaci na karni 16 da ’yan Hindu suka lalata a shekarar 1992. Rugujewar ta haifar da tarzoma a fadin kasar inda kusan mutane 2,000 suka mutu.
Sai dai mafi yawan ‘yan adawar sun kaurace wa zaben, suna masu cewa Modi yana amfani da shi ne don cimma wata manufa ta siyasa.
Za a gudanar da babban zabe a Indiya nan da ‘yan watanni masu zuwa kuma ‘yan hamayyar siyasar Mr Modi sun ce jam’iyyar Bharatiya Janata (BJP) mai mulki za ta nemi kuri’u da sunan haikalin a kasar da kashi 80% na al’ummar kasar Hindu ne.
An dauki tsawon lokaci ana gwabza fada game da mallakar fili ya biyo bayan rushewar masallacin. An warware shi a cikin 2019 lokacin da Kotun Koli ta ba Hindu filin da ake takaddama a kai. An bai wa musulmi fili a wajen birnin domin gina masallaci.
A Ayodhya, wasu musulmi sun ce gabanin taron cewa ranar ta jawo musu tsoro da tunani mai raɗaɗi. Wasu sun ce za su kori ‘ya’yan su daga cikin birnin, saboda fargabar tashin hankali yayin da tituna suka cika makil da mabiya addinin Hindu daga sassan kasar.
BBC/Ladan Nasidi.